A cewar rahoton sashen ƙasa da ƙasa na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza daga shafin Facebook na Dandalin Matasa, a ranar Lahadi, 10 ga Mayu 2026, aka rufe taron ƙara wa juna sani (Mu'utamar), wanda Dandalin Matasan Harkar Musulunci na Rasulul Akram Zone (Kano) ta shira mai taken 'Gina Shaksiyar Matashi ɗan gwagwarmaya' na kwanaki biyu wanda aka gabatar a garin Ɓagwai dake ƙaramar hukumar Ɓagwai ta Jahar Kano.
Malam Imamu Kurna shi ne wanda ya yi jawabin rufe taron, inda a jawabin sa yake cewa: "A duniya mutum yake zama mutum. Allah ya halicce mu ya zubo mu wannan duniya ne domin mu bauta masa. Don haka kyawawan ayyuka ne zasu tsabtace ruhin ka, ka bautawa Allah."
Da yake jan hankalin matasan kan taimakawa addini kuwa, Malam Imamu ya ce: "Duk abun da ka ke ganin abun birgewa ne a duniya, a ranar lahira shi ne fitina. Idan Allah ya yi maka Ilimi baka taimaki addini da shi ba, ranar lahira za ka yi da-na-sani."
Ya kara da cewa: "Idan Allah ya yi maka dukiya baka taimaki addini da ita ba, za ka yi da-na-sani a lahira. Ka zama mai tsoron Allah — ya zama Allah kaɗai kake tsoro, sannan ya kamata Matashi ya zama wayayye, Matashi zai zama wayayye ne, na farko ya zama yana da alaƙa da Allah. Ilimi da basira".
Da yake gabatar da nasa jawabin, Alhaji Adam Umar (Alhaji Ado Matasa) akan Maudu'i mai taken: 'Wa ya kamata na Aura?' Ya ke cewa: "Allah ya hore mu da mu auri mace sabo da abu uku; nasabarta, dukiyarta da kyawunta, amma mafi muhimmanci shi ne mu auri ma'abociyar addini. Ta ya zaka gane ma'abociyar addini ? Ana gane ma'abociyar addini ne da kyawawan ɗabi'u, ba da zuwa 'program' ko saka hijabi ake gane ma'abociyar addini ba."
Alhaji Ado Matasa ya ƙara da cewa: "A tattaunawar soyayya a mahimmantar da tattaunawa akan muhimman abubuwa na rayuwa, Ilimi, yadda zaku gina zuri'a da kyautatawa juna. Cikin dare ake tashi a roƙi shahada, a tashi a yi sujuda a yi wa Allah kuka a roƙi shahada bawai a zance ba."
A nata jawabin, Malama Umma Ibrahim Shuwaki da ta yi akan: 'Muhimmancin Hijabi', ta ke cewa: "Asalin baƙin Hijabi ya samo asali ne daga banu Hashim, dangin Manzon Allah (S). Shi ya sa idan muka saka baƙin Hijabi mun yi koyi da su ne, saka Hijabi kare kanmu ne, daraja kanmu ne, mutunta kanmu ne, ni'ima ce da Allah yayi mana."
A nasa jawabin, Alhaji Yusuf Ali Bichi da ya gabatar, ya kawo muhimmanci da matakan da ya kamata Matashi ya ɗauka wajen neman Ilimi, inda ya ke cewa: "Ana ɗaga darajar mutum idan ya yi ilimi, idan mutum ya yi ilimi za ku ga ya fifita acikin al'umma tun a nan duniya, a lahira kuwa matsayin sa daban ne."
Malam ya ƙara da cewa: "A wajenmu Ilimi babu na banbancewa, duk wanda ka yi zaka samu lada; Ilimin addini da na zamani duk wanda ka yi duk ilimi ne, kafun ka kai matakin zama mai ilimi sai ka bi wasu matakai, sai ka zama mai juriya, dakewa, haƙuri mai ƙoƙari da naci."
A ƙarshe Alhaji Yusuf ya rufe da cewa: "Idan mutum ya mutu a tafarkin neman ilimi, ɗan Aljanna ne (Ma'ana Shahidi ne duk wanda ya rasu a hanyar neman ilimi)."
Malam Faɗal Ali a yayin gabatar da nasa jawabin a kan Makarimu Akhlaƙ, ya ke cewa: "Mutum da dabbobi duk sun futo daga abu ɗaya ne, amma saboda a raba mutum da sauran dabbobi sai aka bashi kyawawan ɗabi'u (aklaƙ)."
Akhlaƙ shi ne sanin ayyukan da suke wajibi ne ka aikata su, sannan ka san wanda suke haramun ne ka guje musu," Inji Malam Fadal.
A yayin gabatar da jawabinsa a kan 'Matashi da Social Media,' Malam Muhammad Saƙafa, ya ce: "Tun farko ya kamata Matashi ya tsara wa kansa makoma ta hanyar kafar sadarwa. Matashi zai yi amfani da ita wajen nemawa kansa ilimi da nishaɗi. 'Social Media' hanyoyi ne da ake amfani da su wajen sada zumunci da kuma neman ilimi. 'Social media' tana sauƙaƙa hulɗa tsakanin juna, matasa na iya amfani da ita wajen tattaunawa da sauran ƴan'uwan su matasa. Matasa za su iya tallata fasahar su ko wata baiwa da Allah ya yi musu."
Malam Saƙafa ya ƙara da cewa: "'Social media' ta na da illoli kamar yaɗuwar labaran ƙarya da farfaganda, lalacewar tarbiyya, rashin tsaro da yawaitar bayyana sirri da damfara. Matashi zai iya amfani da kafofin wajen haɓaka sana'a. Ɗalibai suna iya amfani da su wajen tattaunawa."
A taron an gabatar da tattaunawa tsakanin matasa. akan batutuwa daban-daban. Matasa sun gabatar da wasanni da yawon ƙarin ilimi a yayin gabatar da taron.
A yayin rufe taron Matasan da suka karbi maƙuncin taron, Matasan gwarzo 'Zone' sun karrama Alhaji Ado Matasa da hoto wanda ɗaya daga cikin matasan ya zana.








Ra'ayinka